Surah Nooh

Surah Nooh - Hausa Aya count 28

Ya ce: \"Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa.\"
\"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci).\"
Nũhu) ya ce: \"Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini.\"
\"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni).\"
\"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri.\"
\"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne.\"
\"Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?\"
\"Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra.\"
\"Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata.\"
Kuma Nũhu ya ce: \"Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida.\"
\"Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci\"
\"Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka.\"
Share