Surah Al-An'am ( The Cattle ) - Aya 148

Surah Al-An'am ( The Cattle ) - Hausa - Aya 148 Aya count 165

سَيَقُولُ ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ لَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشْرَكْنَا وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمْنَا مِن شَىْءٍۢ ۚ كَذَٰلِكَ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ حَتَّىٰ ذَاقُوا۟ بَأْسَنَا ۗ قُلْ هَلْ عِندَكُم مِّنْ عِلْمٍۢ فَتُخْرِجُوهُ لَنَآ ۖ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنْ أَنتُمْ إِلَّا تَخْرُصُونَ ﴿١٤٨﴾
Waɗanda suka yi shirki zã su ce: \"Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba.\" Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: \"Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi.\"
Share