Select surah 1- Al-Fatihah ( The Opening ) 2- Al-Baqarah ( The Cow ) 3- Al-Imran ( The Famiy of Imran ) 4- An-Nisa ( The Women ) 5- Al-Maidah ( The Table spread with Food ) 6- Al-An'am ( The Cattle ) 7- Al-A'raf (The Heights ) 8- Al-Anfal ( The Spoils of War ) 9- At-Taubah ( The Repentance ) 10- Yunus ( Jonah ) 11- Hud 12- Yusuf (Joseph ) 13- Ar-Ra'd ( The Thunder ) 14- Ibrahim ( Abraham ) 15- Al-Hijr ( The Rocky Tract ) 16- An-Nahl ( The Bees ) 17- Al-Isra ( The Night Journey ) 18- Al-Kahf ( The Cave ) 19- Maryam ( Mary ) 20- Taha 21- Al-Anbiya ( The Prophets ) 22- Al-Hajj ( The Pilgrimage ) 23- Al-Mu'minoon ( The Believers ) 24- An-Noor ( The Light ) 25- Al-Furqan (The Criterion ) 26- Ash-Shuara ( The Poets ) 27- An-Naml (The Ants ) 28- Al-Qasas ( The Stories ) 29- Al-Ankaboot ( The Spider ) 30- Ar-Room ( The Romans ) 31- Luqman 32- As-Sajdah ( The Prostration ) 33- Al-Ahzab ( The Combined Forces ) 34- Saba ( Sheba ) 35- Fatir ( The Orignator ) 36- Ya-seen 37- As-Saaffat ( Those Ranges in Ranks ) 38- Sad ( The Letter Sad ) 39- Az-Zumar ( The Groups ) 40- Ghafir ( The Forgiver God ) 41- Fussilat ( Explained in Detail ) 42- Ash-Shura (Consultation ) 43- Az-Zukhruf ( The Gold Adornment ) 44- Ad-Dukhan ( The Smoke ) 45- Al-Jathiya ( Crouching ) 46- Al-Ahqaf ( The Curved Sand-hills ) 47- Muhammad 48- Al-Fath ( The Victory ) 49- Al-Hujurat ( The Dwellings ) 50- Qaf ( The Letter Qaf ) 51- Adh-Dhariyat ( The Wind that Scatter ) 52- At-Tur ( The Mount ) 53- An-Najm ( The Star ) 54- Al-Qamar ( The Moon ) 55- Ar-Rahman ( The Most Graciouse ) 56- Al-Waqi'ah ( The Event ) 57- Al-Hadid ( The Iron ) 58- Al-Mujadilah ( She That Disputeth ) 59- Al-Hashr ( The Gathering ) 60- Al-Mumtahanah ( The Woman to be examined ) 61- As-Saff ( The Row ) 62- Al-Jumu'ah ( Friday ) 63- Al-Munafiqoon ( The Hypocrites ) 64- At-Taghabun ( Mutual Loss & Gain ) 65- At-Talaq ( The Divorce ) 66- At-Tahrim ( The Prohibition ) 67- Al-Mulk ( Dominion ) 68- Al-Qalam ( The Pen ) 69- Al-Haaqqah ( The Inevitable ) 70- Al-Ma'arij (The Ways of Ascent ) 71- Nooh 72- Al-Jinn ( The Jinn ) 73- Al-Muzzammil (The One wrapped in Garments) 74- Al-Muddaththir ( The One Enveloped ) 75- Al-Qiyamah ( The Resurrection ) 76- Al-Insan ( Man ) 77- Al-Mursalat ( Those sent forth ) 78- An-Naba' ( The Great News ) 79- An-Nazi'at ( Those who Pull Out ) 80- Abasa ( He frowned ) 81- At-Takwir ( The Overthrowing ) 82- Al-Infitar ( The Cleaving ) 83- Al-Mutaffifin (Those Who Deal in Fraud) 84- Al-Inshiqaq (The Splitting Asunder) 85- Al-Burooj ( The Big Stars ) 86- At-Tariq ( The Night-Comer ) 87- Al-A'la ( The Most High ) 88- Al-Ghashiya ( The Overwhelming ) 89- Al-Fajr ( The Dawn ) 90- Al-Balad ( The City ) 91- Ash-Shams ( The Sun ) 92- Al-Layl ( The Night ) 93- Ad-Dhuha ( The Forenoon ) 94- As-Sharh ( The Opening Forth) 95- At-Tin ( The Fig ) 96- Al-'alaq ( The Clot ) 97- Al-Qadr ( The Night of Decree ) 98- Al-Bayyinah ( The Clear Evidence ) 99- Az-Zalzalah ( The Earthquake ) 100- Al-'adiyat ( Those That Run ) 101- Al-Qari'ah ( The Striking Hour ) 102- At-Takathur ( The piling Up ) 103- Al-Asr ( The Time ) 104- Al-Humazah ( The Slanderer ) 105- Al-Fil ( The Elephant ) 106- Quraish 107- Al-Ma'un ( Small Kindnesses ) 108- Al-Kauther ( A River in Paradise) 109- Al-Kafiroon ( The Disbelievers ) 110- An-Nasr ( The Help ) 111- Al-Masad ( The Palm Fibre ) 112- Al-Ikhlas ( Sincerity ) 113- Al-Falaq ( The Daybreak ) 114- An-Nas ( Mankind )
Translations English English - Yusuf Ali English - Transliteration English - Rowwad Translation Center English - Ahmed Ali English - Ahmed Raza Khan English - Arberry English - Daryabadi English - Hilali & Khan English - Talal Itani English - Maududi English - Mubarakpuri English - Pickthall English - Qarai English - Qaribullah & Darwish English - Sarwar English - Shakir English - Wahiduddin Khan Français Español Spanish Cortes Spanish Garcia Português Deutsch German Bubenheim & Elyas German Khoury German Zaidan Italiano Nederlands Dutch Leemhuis Dutch Siregar Русский Russian Абу Адель Russian Аль-Мунтахаб Russian Крачковский Russian Кулиев Russian Османов Russian Порохова Russian Саблуков Română Greek Svenska Shqip Shqip Feti Mehdiu Shqip Sherif Ahmeti Bosanski Bosnian Mlivo Български České České Nykl Norwegian Türkçe Turkish Alİ Bulaç Turkish Çeviriyazı Turkish Diyanet İşleri Turkish Diyanet Vakfı Turkish Edip Yüksel Turkish Elmalılı Hamdi Yazır Turkish Öztürk Turkish Suat Yıldırım Turkish Süleyman Ateş Polski Croatian Georgian Српски українська Macedonian Lithuanian Azəri Azerbaijani Məmmədəliyev & Bünyadov اردو Urdu Maududi Urdu Ahmed Raza Khan Urdu Jalandhry Urdu Qadri Urdu Jawadi Urdu Junagarhi Urdu Najafi 日本語 한국어 中文 Chinese (Traditional) Hindi Hindi Muhammad Farooq Khan മലയാളം Malayalam Karakunnu & Elayavoor தமிழ் Melayu Indonesian Indonesian Quraish Shihab Indonesian Tafsir Jalalayn বাংলা জহুরুল হক فارسى كوردی Pashto Тоҷикӣ Татарча ไทย ئۇيغۇرچە Ўзбек Uzbek Mikhailo Yakuboych ދިވެހި Sindhi অসমীয়া Bisayan Iranun Maguindanaon Dari Hebrew қазақ тілі Khmer Marathi Hausa soomaali Swahili Afar N'ko Akan Chewa Dagbani Kinyarwanda Lingala Luganda Luhya Malagasy Mõõré Yaw Amazigh Amharic
Your browser does not support the audio element. ¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: \"Wannan wani abu ne mai ban mãmãki.\"
\"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa.\"
Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa.
Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
(Sai a ce masa): \"Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne.\"
Kuma abõkin haɗinsa ya ce: \"Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce.\"
(A ce wa Malã'iku), \"Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai.\"
\"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka.\"
\"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani.\"
Abõkin haɗinsa ya ce: \"Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa.\"
Ya ce: \"Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku.\"
\"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa.\"
Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama \"Shin, kin cika?\" Kuma ta ce: \"Ashe, akwai wani ƙãri?\"
Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
\"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
\"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali.\"
(A ce musu) \"Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama.\"
Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu).
Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci.
Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.