Surah Al-Maidah ( The Table spread with Food ) - Aya 19

Surah Al-Maidah ( The Table spread with Food ) - Hausa - Aya 19 Aya count 120

يَٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَٰبِ قَدْ جَآءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ عَلَىٰ فَتْرَةٍۢ مِّنَ ٱلرُّسُلِ أَن تَقُولُوا۟ مَا جَآءَنَا مِنۢ بَشِيرٍۢ وَلَا نَذِيرٍۢ ۖ فَقَدْ جَآءَكُم بَشِيرٌۭ وَنَذِيرٌۭ ۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍۢ قَدِيرٌۭ ﴿١٩﴾
Yã Mutãnen Littãfi! Lalle ManzonMu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: \"wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba.\" To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi.
Share