Surah Al-Fath ( The Victory ) - Aya 15

Surah Al-Fath ( The Victory ) - Hausa - Aya 15 Aya count 29

سَيَقُولُ ٱلْمُخَلَّفُونَ إِذَا ٱنطَلَقْتُمْ إِلَىٰ مَغَانِمَ لِتَأْخُذُوهَا ذَرُونَا نَتَّبِعْكُمْ ۖ يُرِيدُونَ أَن يُبَدِّلُوا۟ كَلَٰمَ ٱللَّهِ ۚ قُل لَّن تَتَّبِعُونَا كَذَٰلِكُمْ قَالَ ٱللَّهُ مِن قَبْلُ ۖ فَسَيَقُولُونَ بَلْ تَحْسُدُونَنَا ۚ بَلْ كَانُوا۟ لَا يَفْقَهُونَ إِلَّا قَلِيلًۭا ﴿١٥﴾
Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, \"Ku bar mu, mu bĩ ku.\" Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: \"Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka.\" Sa'an nan zã su ce: \"Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne.\" Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan.
Share