Surah Al-Baqarah ( The Cow ) - Aya 60

Surah Al-Baqarah ( The Cow ) - Hausa - Aya 60 Aya count 286

۞ وَإِذِ ٱسْتَسْقَىٰ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِۦ فَقُلْنَا ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْحَجَرَ ۖ فَٱنفَجَرَتْ مِنْهُ ٱثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْنًۭا ۖ قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍۢ مَّشْرَبَهُمْ ۖ كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ مِن رِّزْقِ ٱللَّهِ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ ﴿٦٠﴾
Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; \"Ka dõki dũtsen da sandarka.\" Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. \"Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna.\"
Share