Surah Al-Baqarah ( The Cow ) - Aya 258

Surah Al-Baqarah ( The Cow ) - Hausa - Aya 258 Aya count 286

أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِى حَآجَّ إِبْرَٰهِۦمَ فِى رَبِّهِۦٓ أَنْ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلْمُلْكَ إِذْ قَالَ إِبْرَٰهِۦمُ رَبِّىَ ٱلَّذِى يُحْىِۦ وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا۠ أُحْىِۦ وَأُمِيتُ ۖ قَالَ إِبْرَٰهِۦمُ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَأْتِى بِٱلشَّمْسِ مِنَ ٱلْمَشْرِقِ فَأْتِ بِهَا مِنَ ٱلْمَغْرِبِ فَبُهِتَ ٱلَّذِى كَفَرَ ۗ وَٱللَّهُ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴿٢٥٨﴾
Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: \"Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa.\" Ya ce: \"Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa.\" Ibrãhĩm ya ce: \"To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma.\" Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Share