Hausa
Surah Al-A'la ( The Most High ) - Aya count 19
Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.