Hausa
Surah Nooh - Aya count 28
Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni."
"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
"Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
"Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna."
"Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
"Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
"Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
"Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
"Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
"Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
"Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
"Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
"Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
"Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra."
"Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata."
Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
"Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
"Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka."