Hausa

Surah At-Talaq ( The Divorce ) - Aya count 12
Share
Sa'an nan idan sun isa ga ajalinsu (na idda) sai ku riƙe su da abin da aka sani kõ ku rabu da su da abin da aka sani kuma ku shaidar da mãsu adalci biyu daga gare ku. Kuma ku tsayar da shaidar dõmin Allah. Wancan ɗinku anã yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yanã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita.
Wancan umurnin Allah ne, Ya saukar da shi zuwa gare ku. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Ya girmama masa sãkamako.
Kuma da yawa daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.
Sa'an nan ta ɗanɗana masĩfar al'amarinta. kuma ƙarshen al'amarinta ya kasance hasãra,