Hausa

Surah An-Najm ( The Star ) - Aya count 62
Share
Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).
Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.
Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).
Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.
Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.
Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?
Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?
Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.
Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.
Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?