Hausa

Surah Al-Hujurat ( The Dwellings ) - Aya count 18
Share
Kuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu.
"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."
Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.