Hausa

Surah Muhammad - Aya count 38
Share
Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange mutãne daga tafarkin Allah, (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
Kuma waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi ĩmani da abinda aka sassaukar ga Muhammadu, alhãli kuwa shĩ ne gaskiya daga Ubangijinsu, (Allah) Yã karkare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu.
Sabõda haka idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta, sai ku yi ta dũkan wuyõyinsu har a lõkacin da suka yawaita musu kisa, to, ku tsananta ɗaurinsu sa'an nan imma karimci a bãyan' haka kõ biyan fansa, har yãƙi ya saukar da kayansa mãsu nauyi. Wancan, dã Allah nã so da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaƙin ba) kuma amma (ya wajabta jihadi) dõmin Ya jarraba sãshenku da sãshe. Kuma waɗanda zaka kashe a cikin tafarkin Allah, to, bã ai ɓatar da ayyukansu ba.
Kuma waɗanda suka kãfirta, to, ruɓushi ya tabbata a gare su, kuma (Allah) Ya ɓatar da ayyukansu.
Lalle ne, Allah nã shigar da waɗanda suka yi ĩmani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jin ɗan daɗi (adũniya) kuma sunã ci, kamar yadda dabbõbi ke ci, kuma wutã ita ce mazauni a gare su.
Kuma da yawa akwai alƙarya, ita ce mafi tsanani ga ƙarfi daga alƙaryarka wadda ta fitar da kai, Mun halaka ta, sa'an nan kuwa bãbu wani mai taimako a gare su.
Misãlin Aljanna, wadda aka yi wa'adinta ga mãsu taƙawa, a cikinta akwai waɗansu kõguna na ruwa ba mai sãkẽwa ba da waɗansu kõguna na madara wadda ɗanɗanonta bã ya canjãwa, da waɗansu kõguna na giya mai dãɗi ga mashãya, da waɗansu kõguna na zuma tãtacce kuma suna sãmu, a cikinta, daga kõwane irin 'ya'yan itãce, da wata gãfara daga Ubangijinsu. (Shin, mãsu wannan ni'ima nã daidaita) kamar wanda yake madawwami ne a cikin wutã kuma an shãyar da su wani ruwa mai zãfi har ya kakkãtse hanjinsu?
Kuma waɗannan da suka nẽmi shiryuwa (Allah) Ya ƙara musu shiryuwarsu, kuma Yã bã su (sakamakon) taƙawarsu.
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cẽwa: "Don mẽne ne ba a saukar da wata sũra ba? "To idan aka saukar da wata sũra, bayyananna, kuma aka ambaci yãƙi a cikinta, zã ka ga waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu sunã kallo zuwa gare ka, irin kallon wanda aka rufe da mãgãgi sabõda mutuwa. To, abin da yake mafĩfĩci a gare su:
Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba?
Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su.
Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba.
Dã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku.
Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba.