Hausa
Surah Al-Jathiya ( Crouching ) - Aya count 37
Saukar Littãfi daga Allah Mabuwãyi Mai hikima yake.
Lalle ne a cikin sammai da ƙasa akwai ãyõyi ga mãsu ĩmãni.
Kuma a cikin halittarku da abin da ke watsuwa na dabba akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yaƙĩni.
Kuma da sãɓawar dare da yini da abin da Allah Ya saukar daga sama na arziki, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa game da shi a bãyan mutuwarta, da jũyawar iskõki, akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.
Waɗancan ãyõyin Allah ne, Munã karanta su gare ka da gaskiya. To, da wane lãbãri bãyan Allah da ãyõyinSa suke yin ĩmãni?
Bone ya tabbata ga dukan mai yawan ƙiren ƙarya, mai laifi.
Yanã jin ãyõyin Allah anã karanta su a kansa, sa'an nan ya dõge yanã makãngari, kamar bai jĩ su ba. To, ka yi masa bushara da azãba mai raɗaɗi.
Kuma har idan ya san wani abu daga ãyõyinMu, sai ya rika su da izgili. Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa (a dũniya).
Gaba gare su (a Lãhira) akwai Jahannama, kuma abin da suka sanã'anta bã ya wadãtar da su daga kõme, kuma abũbuwan da suka riƙa majiɓinta, baicin Allah, bã su wãdatar da su daga kõme. Kuma sunã da wata azãba mai girma.
Wannan (Alƙur'ãni) shi ne shiryuwa. Kuma waɗanda suka kãfirta game da ãyõyin Ubangijinsu, sunã da wata azãba ta wulãkanci mai raɗaɗi.
Allah ne wanda Ya hõre muku tẽku dõmin jirgi ya gudãna a cikinta da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalarSa, kuma tsammãninku zã ku gõde.
Kuma Ya hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasa, gabã ɗaya daga gare Shi yake. Lalle ne, a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.
Ka ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, su yi gãfara ga waɗanda bã su fãtan rahama ga kwãnukan Allah, dõmin (Allah) Ya sãka wa mutãne da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, dõmin kansã, kuma wanda ya mũnana aki, to, a kansa. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku.
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai (wa Bãnĩ Isrã'ĩla Littãfi da hukunci da Annabci, Kuma Mun azurta su daga abũbuwa mãsudãɗi, Kuma Mun fĩfta su a kan mutãnen dũniya (a zãmaninsu).
Kuma Muka bã su hujjõji na umurni. Ba su sãɓa ba fãce bãyan ilmi ya jẽ musu, sabõda zãlunci a tsakãninsu. Lalle ne, Ubangijinka zai yi hukunci a tsakãninsu, a Rãnar ƙiyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa (jũna).
Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin. Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba.
Lalle ne sũ, bã zã su wadãtar da kai da kõme ba daga Allah. Kuma lalle ne azzãlumai sãshensu majiɓintan sãshe ne. Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa.
wannan (Alkur'ãni) hukunce-hukuncen natsuwa ne ga mutãne, da shiryuwa, da rahama, ga mutãne waɗanda ke da yaƙĩni.
Kõ waɗanda suka yãgi miyãgun ayyuka sunã zaton Mu sanyã su kamar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, su zama daidai ga rãyuwarsu da mutuwarsu? Abin da suke hukuntãwa yã mũnanã!
Alhãli kuwa Allah ne Ya halitta sammai da ƙasã sabõda gaskiya, Kuma dõmin a sãka wa kõwane rai da abin da ya sanã'anta, kuma su, bã zã a zãlunce su ba.
Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?
Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.
Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
Ka ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
"Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra."
Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
"Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa."
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne.
Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?"
"Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'
Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.
Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako.
"Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba."
Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu.
Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima.