Hausa

Surah As-Sajdah ( The Prostration ) - Aya count 30
Share
Kõ sunã cẽwa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? Ã'a, shĩ ne gaskiya daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabãninka, fãtan zã su shiryu.
Kuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasã, shin, lalle mu, tabbas ne munã zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Ã'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kãfirai
Ka ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku."
Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne."
To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai.
Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi.
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi, sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla.
Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurninMu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyinMu.
Lalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa.
Kuma sunã cẽwa, "Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya?"
Ka ce: "Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba."
Sabõda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, sũ ma mãsu jira ne.