Hausa
Surah Hud - Aya count 123
A. L̃.R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa'an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.
Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi.
Kuma ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma'abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku.
Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõmeMai ĩkon yi ne.
To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓẽwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.
Kuma bãbu wata dabba a cikin ƙasa fãce ga Allah arzikinta yake, kuma Yanã sanin matabbatarta da ma'azarta, duka sunã cikin littãfi bayyananne.
Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma haƙĩƙa idan ka ce: "Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa," haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne."
Kuma lalle ne idan Mun jinkirta da azãba gare su zuwa ga wani lõkaci ƙidãyayye, haƙĩƙa sunãcẽwa me yake tsare ta? To, a rãnar da zã ta je musu, ba ta zama abin karkatarwa ba daga gare su. Kuma abin da suka kasance suna yin izgili da shi, yã wajaba a kansu.
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sa'an nan kuma Muka zãre ta daga gare shi, lalle ne shĩ, hakĩka, mai yanke tsammãnine, mai yawan kãfrci.
Kuma lalle ne idan Mun ɗanɗana masa ni'ima a bãyan cũta ta shãfe shi, Yana cẽwa mũnanan halaye sun tafi daga wurina. Lalle shi mai farin ciki ne, mai alfahari.
Sai waɗanda suka yi haƙuri kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai. Waɗannan sunã da gãfara da lãda mai girma.
Sabõda haka tsammãninka kai mai barin sãshen abin da aka yi wahayi zuwa gare ka ne, kuma mai ƙuntata ƙirjinka da shi ne dõmin sun ce: "Dõmin me ba a saukar masa da wata taska ba, kõ kuma Malã'ika ya zo tãre de shi?" Kai mai gargaɗi ne kawai. Kuma Allah ne wakili a kan kõme.
Kõ sunã cewa: "Yã ƙirƙira shi ne."Ka ce: "Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya."
To, idan ba su amsa muku ba, to, ku sani cẽwa an saukar da shi kawai ne da sanin Allah, kuma cẽwa bãbu abin bauta wa fãce Shi. To, shin, kũ mãsu sallamãwa ne?,
Wanda ya kasance yã yi nufin rãyuwar dũniya da ƙawarta, Munã cika musu ayyukansu zuwa gare su a cikinta, kuma a cikinta bã zã a rage su ba.
Waɗannan ne waɗanda bã su da kõme a cikin Lãhira fãce wuta, kuma abin da suka sanã'anta a cikinta (dũniya) yã ɓãci, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa ɓãtacce ne.
Shin, wanda ya kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijinsa, kuma wata shaida tanã biyar sa daga gare Shi, kuma a gabãninsa akwai littãfin Mũsãabin kõyi da rahama? Waɗannan sunã yin ĩmãni da shi, kuma wanda ya kãfirta da shi daga ƙungiyõyi, to, wutã ce makõmarsa. Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga gare shi. Lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka, amma kuma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.
Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah? Waɗannan anã gitta su ga Ubangijinsu, kuma mãsu shaida su ce: "Waɗannan ne suka yi ƙarya ga Ubangijinsu. To, la'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."
Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah kuma sunã nẽman ta karkace, kuma sũ ga Lãhira sunã kãfirta.
Waɗannan ne ba su kasance mabuwãya ba a cikin ƙasa, kuma waɗansu masõya ba su kasance ba a gare su, baicin Allah. Anã ninka musu azãba, ba su kasance sunã iya ji ba, kuma ba su kasance sunã gani ba.
Waɗannan ne wɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirawa ya ɓace musu.
Bãbu makawã cẽwa, haƙĩƙa, sũ a lãhira, sũ ne mafi hasãra.
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi tawãlu'i zuwa ga Ubangijinsu, waɗannan ne abõkan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.
Misãlin ɓangaren biyu kamar makãho ne da kurmã, da mai gani da mai ji. Shin, sunã daidaita ga misãli? Ashe, bã ku yin tunãni?
Kuma haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutanensa, (ya ce): "Lalle ne ni, a gare ku mai gargaɗi bayyananne ne."
"Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ, inã jin tsõron azãbar yini mai raɗaɗi a kanku."
Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta, daga mutãnensa, suka ce: "Bã mu ganin ka fãce mutum kake kamarmu, kuma ba mu ganin wani ya bĩ ka fãce waɗanda suke sũ ƙasƙantattunmu ne marasa tunani. Kuma bã mu ganin wata falalã agare ka a kanmu. Ã'a, Munã zaton ku maƙaryata ne."
Ya ce: "Ya mutãnena! Shin, kun gani idan na kasance a kan wata hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Yã bã ni wata Rahama daga wurinSa, Sa'an nan aka rufe ta (ita Rahamar) daga gare ku, shin, zã mu tĩlasta mukuita, alhãli kuwa kũ mãsu ƙi gare ta ne?
"Kuma yã mutãnena! Bã zan tambaye ku wata dũkiya ba akansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce daga Allah, kuma ban zama mai kõrar waɗanda suka yĩ ĩmãni ba. Haƙĩƙa sũ, mãsu haɗuwa da Ubangijinsu ne, kuma amma ni, inã ganin ku mutãne ne jãhilai."
"Kuma ya mutãnena! Wãne ne yake taimakõna daga Allah idan na kõre su? Ashe, bã ku tunãni?"
"Kuma bã ni ce muku a wurĩna taskõkin Allah suke kuma bã inã sanin gaibi ba ne. Kuma ba inã cẽwa ni Malã'ika ba ne. Kuma ba ni cẽwa ga waɗanda idãnunku suke wulãkantãwa, Allah bã zai bã su alhẽri ba. Allah ne Mafi sani ga abin da yake cikin zukatansu. Lalle ne ni, idan (nã yi haka) dã ina daga cikin azzalumai."
Suka ce: "Yã Nũhu, lalle ne kã yi jayayya da mu, sa'an nan kã yawaita yi mana jidãli, to, ka zõ mana da abin da kake yi mana wa'adi idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
Ya ce: "Allah kawai ne Yake zo muku da shi idan Ya so. Kuma ba ku zama mabuwãya ba."
"Kuma nasĩhãta bã zã ta amfãne ku ba, idan nã yi nufin in yi muku nasĩha, idan Allah Yakasance Yanã nufin Ya halaka ku. Shĩ ne Ubangijinku, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku."
Ko sunã cẽwa: (Nũhu) ya ƙirƙira shi. Ka ce: "Idan nĩ (Nũhu) na ƙirƙira shi to, laifĩnã a kaina yake, kuma nĩ mai barrantã ne daga abin da kuke yi na laifi."
Kuma aka yi wahayi zuwa ga Nũhu cẽwa: Lalle ne bãbu mai yin ĩmãni daga mutãnenka fãce wanda ya riga ya yi ĩmãnin, sabõdahaka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
Kuma ka sassaƙa jirgi da kyau a kan idanunMu da wahayinMu, kuma kada ka yi Mini magana a cikin sha'anin waɗanda suka kãfirta, lalle ne sũ, waɗanda akenutsarwa ne.
Kuma Yanã sassaƙa jirgin cikin natsuwa, kuma a kõ yaushe waɗansu shugabanni daga mutãnensa suka shũɗe a gabansa, sai su yi izgili gare shi. Ya ce: "Idan kun yi izgili gare mu, to, haƙĩƙa mũ mã zã mu yi izgili gare ku, kamar yadda kuke yin izgili.
"Sa'an nan da sannu zã ku san wanda azãba zã ta zo masa, ta wulakantã shi (a dũniya), kuma wata azãba zaunanna ta sauka a kansa (a Lãhira)."
Har a lõkacin da umurninMu ya je, kuma tandã ta ɓulɓula. Muka ce: "Ka ɗauka, a cikinta, daga kõme, ma'aura biyu, da kuma iyalanka, fãce wanda magana ta gabãta a kansa, da wanda ya yi ĩmãni." Amma kuma bãbu waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi fãce kaɗan."
Kuma ya ce: "Ku hau a cikinta, da sũnan Allah magudãnarta da matabbatarta. Lalle ne Ubangijĩna, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
Kuma ita tanã gudãna da su a cikin tãguwar ruwa kamai duwãtsu, sai Nũhu ya kirãyi ɗansa alhãli, kuwa ya kasance can wuri mai nĩsa. "Yã ƙaramin ɗãnã! zo ka hau tãre da mu, kuma kada ka kasance tãre da kãfirai!"
Ya ce: "Zan tattara zuwa ga wani dũtse ya tsare ni daga ruwan." (Nũhu) ya ce: "Bãbu mai tsarẽwa a yau daga umurnin Allah fãce wanda Ya yi wa rahama." Sai taguwar ruwa ta shãmakace a tsakãninsu, sai ya kasance daga waɗanda aka nutsar.
Kuma aka ce: "Yã ƙasa! Ki haɗiye ruwanki, kuma yã sama! Ki kãme."Kuma aka faƙar da ruwan kuma aka hukunta al'amarin, kuma Jirgin ya daidaita a kan Jũdiyyi, kuma aka ce: "Nĩsa ya tabbata ga mutãne azzãlumai."
Kuma Nũhu ya kira Ubangijinsa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne ɗãna na daga iyãlĩna! Kuma haƙĩƙa wa'adinKa gaskiya ne, kuma Kai ne Mafi hukuncin mãsu yin hukunci."
Ya ce: "Yã Nũhu! Lalle ne shi bã ya a ciki iyãlanka, lalle ne shĩ, aiki ne wanda ba na ƙwarai ba, sabõda haka kada ka tambaye Ni abin da bã ka da ilmi a kansa. Haƙĩƙa, Nĩ Inã yi maka gargaɗi kada ka kasance daga jãhilai."
Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra."
Aka ce: "Ya Nũhu! Ka sauka da aminci da, a gare Mu da albarka a kanka, kuma rahama ta tabbata a kan waɗansu al'ummõmi daga waɗanda suke tãre da kai. Da waɗansu al'ummõmi da zã Mu jiyar da su dãɗi, sa'an nan kuma azãba mai raɗaɗi ta shafe su daga gare Mu."
Waccan ƙissa tanã daga lãbãran gaibi, Munã yin wahayinsu zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance kanã sanin su ba, haka kuma mutãnenka ba su sani ba daga gabãnin wannan. Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa,
Kuma zuwa ga Ãdãwa, (Mun aika) ɗan'uwansu Hũdu. Ya ce: "Yã kũ mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Ba ku kasance ba fãce kunã mãsu ƙirƙirãwa.
"Yã ku mutãnena! Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, ijãrata ba ta zama ba, fãce ga wanda Ya ƙãga halittata. Shin fa, bã ku hankalta?"
"Kuma, ya mutãnena! Ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi, zai saki sama a kanku, tanã mai yawan zubar da ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi ga ƙarfinku. Kuma kada ku jũya kunã mãsu laifi."
Suka ce: "Yã Hũdu! Ba ka zo mana da wata hujja bayyananna ba, kuma ba mu zama mãsu barin abũbuwan bautawarmu ba dõmin maganarka, kuma ba mu zama mãsu yin ĩmãni da kai ba."
"Bã mu cẽwa, sai dai kurum sashen abũbuwan bautawarmu ya sãme ka da cũtar hauka." Yace: "Lalle ne nĩ, inã shaida waAllah, kuma ku yi shaidar cẽwa" lalle ne nĩ mai barranta ne dagb abin da kuke yin shirki da shi."
"Baicin Allah: Sai ku yi mini kaidi gabã ɗaya, sa'an nan kuma kada ku yi mini jinkiri."
"Haƙĩƙa, ni na dõgara ga Allah, Ubangijĩna kuma Ubangijinku. Bãbu wata dabba fãce Shi ne Mai riko ga kwarkwaɗarta. Haƙĩƙa, Ubangijĩna Yanã (kan) tafarki madaidaici."
"To! Idan kun jũya, haƙĩƙa, nã iyar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijĩna Yanã musanya waɗansu mutãne, waɗansunku su maye muku. Kuma bã ku cũtar Sa da kõme. Lalle Ubangijina a kan dukkan kõme, Matsari ne."
Kuma a lõkacin da umurninmu ya je, Muka kuɓutar da Hũdu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõdawata rahama daga gare Mu. Kuma Muka kuɓutr da su daga azãba mai kauri.
Haka Ãdãwa suka kasance, sun yi musun ãyõyin Ubangijinsu, kuma sun sãɓa wa ManzanninSa, kuma sun bi umurnin dukan mai girman kai, makangari.
Kuma an biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. To! Lalle ne Ãdãwa sun kãfirta da Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Ãdãwa, mutãnen Hũdu!
Kuma zuwa ga Samũdãwa (an aika) ɗan'uwansu Sãlihu. Ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa fãce Shi. Shĩ ne Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma Ya sanya ku mãsu yin kyarkyara a cikinta. Sai ku nẽme Shi gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare Shi. Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karɓãwa."
Suka ce: "Ya Sãlihu! Haƙĩƙa, kã kasance a cikinmu, wanda ake fatan wani alhẽri da shi a gabãnin wannan. Shin kana hana mu bauta wa abin da ubanninmu suke bauta wa? Kuma haƙĩƙa mũ, munã cikin shakka daga abin da kake kiran mu gare shi, mai sanya kõkanto."
Ya ce: "Ya mutãnẽna! Kun gani? Idan na kasance a kan hujja bayyananna daga Ubangijina, kuma Ya bã ni rahama daga gare Shi, to, wane ne zai taimake ni daga Allah idan nã sãɓa Masa? Sa'an nan bã zã ku ƙãre ni da kõme ba fãce hasãra."
"Kuma ya mutãnena! wannan rãƙumar Allah ce, tanã ãyã a gare ku. Sai ku bar ta ta ci a cikin ƙasar Allah, kuma kada ku shãfe ta da wata cũta kar azãba makusanciya ta kãma ku."
Sai suka sõke ta. Sai ya ce: "Kuji dãɗi a cikin gidãjenku kwãna uku. Wannan wa'adi ne bã abin ƙaryatãwa ba."
To, a lõkacin da umurninMu ya je, muka kuɓutar da Sãlihu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare Mu, kuma daga wulãkancin rãnar nan. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMai ƙarfi, Mabuwãyi.
Sai tsãwa ta kãma waɗanda suka yi zãlunci, sai suka wãyi gari sunã guggurfãne a cikin gidãjensu.
Kamar dai ba su zauna a cikinta ba. To! Lalle ne samũdãwa sun kãfirce wa Ubangijinsu. To, Nĩsa ya tabbata ga Samũdãwa.
Kuma haƙĩƙa, manzanninMu sun je wa Ibrãhim da bushãra suka ce: "Aminci." Ya ce: "Aminci (ya tabbata a gare ku)." Sa'an nan bai yi jinkiri ba ya je da maraƙi ƙawãtacce.
Sa'an nan a lõkacin da ya ga hannayensu bã su sãduwa zuwa gare shi (maraƙin), sai ya yi ƙyãmarsu, kuma ya ji tsõronsu. Suka ce, "Kada kaji tsõro lalle ne mũ, an aiko mu ne zuwa ga mutãnen Lũɗu"
Kuma mãtarsa tanã tsaye. Ta yi dãriya. Sai Muka yi mata bushãra (da haihuwar) Is'hãƙa, kuma a bayan Is'hãƙa, Yãƙũbu.
Sai ta ce: "Yã kaitõna! Shin, zan haihu ne alhãli kuwa inã tsõhuwa, kuma ga mijĩna tsõho ne? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmãki."
Suka ce: "Shin kinã mãmaki ne daga al'amarin Allah? Rahamar Allah da albarkarSa su tabbata a kanku, ya mutãnen babban gida! Lalle ne Shĩ abin gõdewa ne, Mai girma."
To, a lõkacin da firgita ta tafi daga Ibrãhĩm, kuma bushãra tã je masa, Yanã mai jayayya a gare Mu, sabõda mutãnen Lũɗu!
Lalle Ibrãhĩm, haƙĩƙa mai haƙuri ne, mai yawan addu'a, mai tawakkali.
Ya Ibrãhĩm! Ka bijira daga wannan. Lalle shi, haƙĩƙa, umurnin Ubangijinka ne ya zo, kuma lalle ne sũ, abin da yake mai je musu azãba ce wadda bã a iya hanãwa.
Kuma a lõkacin da manzanninMu suka je wa Lũɗu aka ɓãta masa rai game da su, ya, ƙuntata rai sabõda su. Ya ce: "Wannan yini ne mai tsananin masĩfa."
Kuma mutãnensa suka je masa sunã gaggãwa zuwa gare shi, kuma a gabãni, sun kasance sunã aikatãwar mũnãnan ayyuka. Ya ce: "Yã mutãnẽna! waɗannan, 'yã'yã na sũ ne mafiya tsarki a gare ku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku wulãkantã ni a cikin bãƙĩna. Shin, bãbu wani namiji shiryayye daga gare ku?"
Suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kã sani, bã mu da wani hakki a cikin 'ya'yanka, kuma lalle kai haƙĩƙa, kanã sane da abin da muke nufi."
Ya ce: "Dã dai inã da wani ƙarfi game da ku, kõ kuwa inã da gõyon bãya daga wani rukuni mai ƙarfi?"
(Manzannin) Suka ce: "Yã Lũɗu! Lalle mũ, manzannin Ubangijinka ne. Bã zã su iya sãduwa zuwa gare ka ba. Sai ka yi tafiyarka a wani yankin dare da iyãlinka, kuma kada wani daga gare ku ya waiwaya fãce mãtarka. Lalle ne abin da ya same su mai sãmunta ne. Lalle wa'adinsu lõkacin sãfiya ne. Shin lõkacin sãfiya bã kusa ba ne?"
Sa'an nan a lõkacin da umurninMu ya je, Muka sanya na samanta ya zama na ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu a kanta (ƙasar Lũɗu) daga taɓocũrarre.
Alamtacce a wurin Ubangijinka. Kuma ita (ƙasar Lũɗu) ba ta zama mai nĩsa ba daga azzãlumai (kuraishãwa).
Kuma zuwa ga Madyana (Mun aika) ɗan'uwansu Shu'aibu. Ya ce: "Ya Mutãnena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautãwa fãce shi kuma kada ku rage mũdu da sikẽli. Lalle nĩ, inã ganin ku da wadãta. Kuma lalle inã ji muku tsõron azãbar yini mai kẽwayẽwa."
"Ya mutãnẽna! Ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, kuma kada ku naƙasta wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi ɓarnã a cikin ƙasa kunã mãsu fasãdi."
"Falalar Allah mai wanzuwa ita ce mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance muminai, kuma ni bã mai tsaro ne a kanku ba."
Suka ce: "Yã Shu'aibu! Shin sallarka ce take umurtar ka ga mu bar abin da ubanninmu suke bautãwa, kõ kuwa mu bar aikata abin da muke so a cikin dũkiyõyinmu? Lalle, haƙĩƙa kai ne mai haƙuri shiryayye!"
Ya ce: "Ya mutãnena! Kun gani idan no kasance a kan hujja bayyananniya daga Ubangijina, kuma Ya azurta nĩ da arzikimai kyãwo daga gare Shi? Kuma bã ni nufin in sãɓa muku zuwa ga abin da nake hana ku daga gare shi. Bã ni nufin kõme fãce gyãrã, gwargwadon da na sãmi dãma. Kuma muwãfaƙãta ba ta zama ba fãce daga Allah. A gare shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi na wakkala."
"Kuma ya mutãnena! Kada sãɓa mini ya ɗauke ku ga misãlin abin da ya sãmi mutãnen Nũhu kõ kuwa mutãnen Hũdu kõ kuwa mutãnen Sãlihu ya sãme ku. Mutãnen Lũɗu ba su zama a wuri mai nĩsa ba daga gare ku."
"Kuma ku nẽmi Ubangijinku gãfara, sa'an nan kuma ku tũba zuwa gare shi. Lalle Ubangijĩna Mai Jin ƙai ne, Mai nũna sõyayya."
Suka ce: "Yã Shu'aibu! Bã mu fahimta da yawa daga abin da kake faɗi, kuma munã ganin ka mai rauni a cikinmu. Kuma bã dõmin jama'arka ba dã mun jẽfe ka, sabõda ba ka zama mai daraja a gunmu ba."
Ya ce: "Ya mutãnena! Ashe, jama'ãta ce mafi daraja a gare ku daga Allah, kuma kun riƙẽ Shi a bãyanku abin jẽfarwa? Lallene Ubangijĩna Mai kẽwayẽwa nega abin da kuke aikatãwa."
"Kuma ya mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku. Lalle nĩmai aiki ne. Da sannu zã ku san wãne ne azãba zã ta zo masa, ta wulakanta shi, kuma wãne ne maƙaryaci. Kuma ku yi jiran dãko, lalle ni mai dãko ne tãre da ku."
Kuma a lõkacin da umurninMu yã je, Muka kuɓutar da Shu'aibu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sabõda wata rahama daga gare, Mu. Kuma tsãwa ta kama waɗanda suka yi zãlunci. Sai suka wãyi gari guggurfãne a cikin gidãjensu.
Kamar ba su zaunã ba a cikinsu. To, halaka ta tabbata ga Madyana kamar yadda Samũdãwa suka halaka.
Kuma haƙĩƙa Mun aiki Mũsã da ãyõyinMu, da dalĩli bayyananne.
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa. Sai suka bi umurnin Fir'auna, amma al'amarin Fir'auna bai zama shiryayye ba.
Yanã shũgabantar mutãnensa a Rãnar Kiyãma, har ya tuzgar da su a wuta. Kuma tir da irin tuzgãwarsu.
Kuma aka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyada Rãnar Kiyãma. Tir da kyautar da ake yi musu.
Wancan Yanã daga lãbãran alƙaryõyi. Munã bã ka lãbãrinsu, daga gare su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe.
Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun zãlunci kansu sa'an nan abũbuwan bautawarsu waɗanda suke kiran su, baicin Allah, ba su wadãtar musu kõme ba a lõkacin da umurnin Ubangijinka ya je, kuma (gumãkan) ba su ƙãra musu wani abu ba fãce hasãra.
Kuma kamar wancan ne kãmun Ubangijinka, idan Ya kãma alƙaryõyi alhãli kuwa sunã mãsu zãlunci. Lalle kamũnSa mai raɗaɗi ne, mai tsanani.
Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga wanda ya ji tsõron azãbar Lãhira. Wancan yini ne wanda ake tãra mutãne a cikinsa kuma wancan yini ne abin halarta.
Ba Mu jinkirtã shi ba fãce dõmin ajali ƙidãyayye.
Rãnar da za ta zo wani rai ba ya iya magana fãce da izninSa. Sa'an nan daga cikinsu akwai shaƙiyyi da mai arziki.
To, amma waɗanda suka yi shaƙãwa, to, sunã a cikin wuta. Sunã mãsu ƙãra da shẽka acikinta.
Suna madawwama a cikinta matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Lalle Ubangijinka Mai aikatãwa ne ga abin da Yake nufi.
Amma waɗanda suka yi arziki to, sunã a cikin Aljanna sunã madawwama, a cikinta, matuƙar sammai da ƙasa sun dawwama, fãce abin da Ubangijinka Ya so. Kyauta wadda bã ta yankẽwa.
Sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga abin da waɗannan suke bautawa. Bã su wata ibãda fãce kamar yadda ubanninsu ke aikatãwa a gabani. Kuma haƙĩƙa Mũ, Mãsu cika musu rabon su ne, bã tãre da nakasãwa ba.
Kuma haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi, sai aka sãɓã wa jũna a cikinsa. Kuma bã dõmin wata kalma wadda ta gabãta daga Ubangijinka ba, haƙĩƙa, dã an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma haƙĩƙa, sunã a cikin wata shakka, game da shi, mai sanya kõkanto.
Kuma lalle, haƙĩƙa, Ubangijinka Mai cika wa kõwa (sakamakon) ayyukansa ne. Lalle Shĩ, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke aikatãwa.
Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa.
Kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfe ku. Kuma bã ku da waɗansu majiɓinta baicin Allah, sa'an nan kuma bã zã a taimake ku ba.
Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.
Kuma ka yi haƙuri. Allah bã Ya tõzartar da lãdar mãsu kyautatãwa.
To, don me mãsu hankali ba su kasance daga mutãnen ƙarnõnin da suke a gabãninku ba, sunã hani daga ɓarna a cikin ƙasa? fãce kaɗan daga wanda Muka kuɓutar daga gare su (sun yi hanin). Kuma waɗanda suka yi zãlunci suka bin abin da aka ni'imtar da su a cikinsa, suka kasance mãsu laifi.
Kuma Ubangijinka bai kasance Yanã halakar da alƙaryu sabõda wani zãlunci ba, alhãli mutãnensu sunã mãsu gyãrãwa.
Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna.
Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya" ta cika.
Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni.
kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, "Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne.
"Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ne."
Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba.